Yanu-yanzu: Kotu ta aika Abdulmalik wanda ya kashe Hanifa gidan gyaran hali tare da wadanda suka taya shi
Kotun majistare mai lamba goma sha biyu 12 ta tura Abdulmalik mutumin da ya yiwa Hanifa kisan gilla tare da wanda ya taimaka masa Tanko da gidan hyaran hali a ranar Litinin.
Kotun mai lamba goma sha biyu 12 ta tura Abdulmalik tare da wadanda suka taya shi aikata wannan laifin gidan gyaran hali, wadanda suka hada da Hashim Isyaku sai kuma wata mace mai suna Fatima.
Alkalin kotun mai suna Mahmud Jibrin ya dage sauraran karar domin bada dama wadan tattara wadatattun bujjoji, tare da fadada bincike kamar tadda gwamnatin jihar kano ta bukata karkashin kwamishina mai shari’a “Musa Lawan”, har zuwa ranar biyu 2 ga watan February kamar yadda ” Freedomradio” ta ruwaito.
Rundunar ‘yan sandan jihar kano ita ta gabatar mutanen da ake zargin a gaban kotu gidan murtala, inda ake tuhumar su da yin garkuwa da yarinya mai shekara 5 mai suna Hanifa Abubakar sannan kuma suka kashe ta hanyar sanya mata guba a cikin abinci.
Tun a ranar 4 ga watan Disambar 2021 ne Abdulmalik Tanko ya yi garkuwa da Hanifa Abubakar a kan hanyarta ta dawowa daga makarantar Islamiyya tare da buƙatar kuɗin fansa da ya kai naira miliyan 6 bayan ya kashe ta.