Advertising
Advertising
Labarai

Masha Allah: An hiwa marayu da marasa galihu sama da 100 kaciya a kyauta a jihar Yobe

Yanzu muka sami wani labarin abin farin ciki kan wani taimako da aka yiwa marayu a jihar Yobe.

Advertising

Sarkin askar fataskun dake jihar Yobe mai suna Dakta Abdullahi, ya yiwa marayu da ‘yayan marasa galihu dari 100 kaciya kyauta a jihar.

Kamar yadda rahotanni suna bayyana cewa, cikin wadan da suka gajiyar tallafin, har da wadanda suke da larurar gani guda 20 da kurame guda biyar 5.

Sarkin askar Dakta Abdullahi wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar wanzamai na shiyar Arewa maso gabas, ya gudanar da kaciyar ne da tallafin sarkin Fika, Alhaji Dakta Muhammad Ibn Abali Idrissa.

Advertising

Kamar yadda Dakta Abdullahi yace, wannan shine karo na biyu game da gudanar da kaciyar kyauta ga marayu da kuma marasa galifu, wanda a shekarar 2020 ya yiwa marayu sama da dari biyu 200 kaciyar kyauta.

Dakta Abdullahi ya kara da cewa, a lokacin da yake zuwa Fataskun yin kaciya wasu iyayan yara suka koka masa kan cewa, akwai wasu yara marayu wanda basu da mai biya musu kudin yin kaciya wanda yaga ya kamata ya yi musu kaciyar kyauta.

A cewar sa, yiwa marayun kaciyar kyauta kamar sadakatul jariya ne, sannan yace duk yaron da aka yiwa kaciya zai iya sa wandon sa nan take.

A lokacin da yake jawabi, sarkin askar Kano kuma shugaban kuma shugaban sarakunan aska na Nageriya, Dakta Muhammad yunusa Nabango, yayi kira ga wanzamai domin su kara jajircewa wajan ganin sun inganta sana’ar su sannan kuma suyi koyi da irin abin da sarkin askar Fataskum din yake yi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button