Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jarumi Ali Nuhu ya shiga tsakanin rigimar jaruma Hafsat Idris da UK Entertaiment bayan sunyi karar ta kotu akan cinye musu kudi

Jarumi Ali Nuhu ya shiga tsakanin rigimar jaruma Hafsat Idris da UK Entertaiment bayan sunyi karar ta kotu akan cinye musu kudi

Tun abaya dai kamfanin “UK Entertaiment” ya shigar da jaruma Hafsat Idris kara kan cewar sun yi jarjejeniyar zata yi masa wani aiki na TV Show a kan kudi naira Miliyan Daya da Dubu Dari Uku, amma ta tsere lamarin da ya sa suka yi karar ta a gaban kotu.

Advertising

Amma a yanzu ficaccan jarumin masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood kuma mai bada umarni Ali Nuhu ya shiga tsakanin dambarwar dake faruwa tsakanin jaruma Hafsat Idris da wani kamfani mai suna “UK Entertaiment”, wand a kwanakin baya ya shigar da ita kara kan wani sadani da suka samu.

To a yanzu kuma jarumi Ali Nuhu ya shiga tsakanin rigimar tasu wanda har an sami sasanto komai ya lafa.

Lauyan kamfanin ya bayyana a gaban kotun a ranar Litinin 24-01-2022 domin cigaba da shari’ar, sai dai ya shaida cewar sun rufe karar biyo bayan sasanto da aka samu a tsakanin su da jarumar, kamar yadda Freedomradio ta ruwaito.

Advertising

Kamfain na “UK Entertaiment” ya nemi jaruma Hafsat Idris ta biya su naira Miliyan Goma a matsayin kudin asarar da ta janyo musu, ta hannun lauyansu Ibrahim Abdulkadir Chedi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button