Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Sahir Abdul jarumi a Fim din Kwana Chasa’in ya bayyana abin Alkharin da Ali Nuhu yay wanda ake yaban sa dashi.

Fitaccen Jarumi a cikin fim din kwana Chasa’in Sahir Abdul ya bayyana wani abin Alkharin da jarumin kannywood Ali Nuhu yayi.

Advertising

Sahir Abdul wanda akafi sani da malan Ali yace wani Abokin sa ne yaji yana fadan wani abun Alkhari da jarumi Ali Nuhu yay kaman yadda zakuga ya rubuta a nan kasan ruburun.

Sahir Abdul: Jiya nake Hira da wani abokina sai yake cemin Abdul walh Ali Nuhu yatabayin wani Abu Wanda yatabani,nake tambayarshi mene yafaru? Sai yace watarana yaga wata yarinya Mai tallan awara tana kuka alamar tayi barin awararta.
Saiga Ali Nuhu yafito Yana zuwa yaga yarinyar tanata sharbar kuka, Nan take yaje har inda yarinyar take yatsaya yake tambayarta shin mene yake faruwa dake? Saitace awaratace ta bare.saiyace to daina kuka kinji,ya dauki kudi masu kauri yace ga wannan rike nabaki duka kije Ammafa kidaina kuka. Bayan Ali Nuhu yashiga mota yatafi sai mutanan wajan sukace wannan kudinda Daya bawa wannan yarinyar fa yanzu yayi aikin wani voice over aka bashi kudin, ko Aljihu Bai saka kudinba ya dauka yabawa wannan yarinyar. Abokina yace shifa tundaga Nan ya sallamawa Ali Nuhu akan gaskiya Wannan mutumin kirkine.

Ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button