Advertising
Advertising
Labarai

Saka hannun gwamna Ganduje a takardar kashe Abdulmalik makashin Hanifa da zarar an kawo masa

Saka hannun gwamna Ganduje a takardar kashe Abdulmalik makashin Hanifa da zarar an kawo masa

Jinjina ga mai girma gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje a lokacin da yaje ta’aziyya gidan su marigayiya Hanifa ya tabbata da cewa.

Advertising

A shirye yake tsaf akan ya sa hannu kan takardar da za’a kawo masa domin yanke hukuncin kisa kai tsaye ga Abdulmalik wanda ya yiwa Hanifa kisan gilla.

Ga lafazin mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje a rubuce.

Mun sami lavarin cewa, kotu zata tabbatar da anyi adalci kundin tsarin mulkin mu ya bukaci cewa idan an yanke hukuncin kisa gwamna na da karfin rattaba hannun a kashe mai laifi.

Advertising

Ina tabbatar muku cewa, bazan bata lokaci ko dakika guda ba.

Haka mai girma gwamna ya fada a yayij da yaje ta’azziya zuwa ga iyayan Hanifa, wannan kalamai na mai girma gwamna sun yiwa al’ummar musulmai dadi domin kuwa gwamna yana da karfin iko na yaki sa hannu akan takarda ko da kuwa kotu ta yanke hukuncin kisa, matukar gwamna bai sa hannun baza’a zartar da hukuncin ba har sai gwamna ya sa hannu.

Shi kuwa gwamna yace bazan bata lokaci ko dakika guda ba, kaga kuwa mai girma gwamna kuwa kawai jira yake a kawo masa takar da ya rattaba hannu.

Da wannan nake muku albishir insha Allahu ta’ala zamuga ranar da za’a kashe wadannan azzalumai musamman ma shi Abdulmalik, amma su abokan aikin nasa bamusan wani irin hukunci kotu zata zartar musu ba amma shikan babu shakka tasa ta kare.

Abin da yake tabbatar da Abdulmalik bazai sha ba yadda al’umma suka karbi abin hannu bibbiyu hatta shugaban kasa ya yi magana a kai mai dakin sa ma tayi magana a kai.

Manya manyan gwamnoni wadan da suka gabata da mai ci na jihar kano sunyi magana akan cewa, zasu tsaya haikan har sai sun tabbatar da anyi adalci an yanke hukuncin da ya dace akan wadannan azzalumai da kusa aikata kisan gilla ga wannan karamar yarinyar wato Hanifa.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button