Advertising
Advertising
Labarai

Yanu-yanzu: Kotu ta aike da Jaruma mai kayan mata gidan gyaran hali kan wasu laifuka data aikata

Yanu-yanzu: Kotu ta aike da Jaruma mai kayan mata gidan gyaran hali kan wasu laifuka data aikata

Jaruma ma kayan mata ta gigita kafar sada zumunta ta lnstagram da cika baki kan yadda ta ke da kafa
da kuma yadda ta san mutane saboda sakin ta da aka yi bayan Ned Nwoko ya sa an kama ta.

Advertising

Biloniya Ned Nwoko ya sa an sake cafke mai
siyar da kayan matan kan zargin ta da ya ke da
cin zarafi a yanar gizo, bata masa suna da sauran laifuka da ake zargin ta da su.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, alkali
ya hana lauyan Jaruma belin ta kuma an aike ta
gidan yari har zuwa ranar Juma’a, 28 ga watan
Janairun 2022.

Fitacciyar mai siyar da kayan mata mai suna Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma,
ta shiga gagarumar matsala da biloniyan dan
kasuwa mai suna “Ned Nwoko”.

Advertising

Bayan sa’o’i kadan kenan da Jaruma mai siyar da kayan matan ta gama cika baki kan yadda ta san mutane da kuma kafar data ke da ita saboda yadda aka sake ta bayan Ned ya sa an damke ta.

Kamar yadda rahotanni suka ruwaito cewa, an sake kama mai Jaruma mai sayar da kayan matan a yanar gizo kuma alkali ya aike ta gidan yarin da ke Suleja.

Daga cikin wasu abubuwan da ake zargin ta da
su sun hada da cin amana, bacin suna, cin zarafl
ta yanar gizo da sauran su.

Za a bincike ta kan wasu Iaifuka, siyar da kayan
mata marasa lasisi, siyar da miyagun kwayoyi
da sauran su.

An gano cewa, Iauyan Jaruma ya bukaci a bayar
da belin ta amma kotun ta hana inda ta aika ta
gidan yari har zuwa ranar Juma’a mai zuwa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button