Bamu muka daddatsa jikin Hanifa ba wahalar data sha ne a cikin buhu yasa ta ragargarje, cewar Abdulmalik
Bamu muka daddatsa jikin Hanifa ba wahalar data sha ne a cikin buhu yasa ta ragargarje, cewar Abdulmalik
Abdulmalik Muhammad Tanko malamin makarantar Noble Kids dake unguwar yan Kaba kwanar Dakata a birnin jihar Kano, ya shaidawa Muryar Amurka cewa.
Ba gaskiya bane labaran da ake yayatawa kan cewa, sun yi gunduwa-gunduwa da jikin Hanifa Abdullahi bayan ta mutu kafin su binne ta.
Abdulmalik wanda ake zargi da garkuwa da Hanifa sannan kuma ya kashe ta ya bayyana cewa, an sa Hanifa a cikin buhu ne wanda ba shi da girma sosai da ya zama dole kafarta ta tankware.
Sannan ya kara da cewa, da yake Hanifa karamar yarinya ce kuma buhun yana da fadi sai aka dan tankwara kafarta yadda dukan jikinta zai shiga buhun amma babu wanda ya dauki wuka ya illata jikinta.
Abdulmalik yace, tankware kafafunwan da aka yiwa Hanifa kafin saka ta a buhun da aka binne ta a ciki, ya sa lokacin da aka tono ta aka ga kamar an karya gababuwanta, amma a zahiri ba wanda ya daddatsa ta ko wani abu makamancin haka.
Ya kara da cewa, an cire rigar sanyin Hanifa da kuma hijabin ta daga jikinta bayan ta mutu aka aikawa iyayenta a matsayin shaida domin neman kudin fansa.
Dangane da lokacin da kuma wurin da Hanifa ta rasu Abdulmalik ya ce, ta kwana biyar a gidanshi tare da iyalinshi kafin ya fitar da ita zuwa wani wuri inda ta kwana daya, kafin ta cika ranar goma ga watan Disamba wato kwana shida bayan yin garkuwa da ita.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sauran bayani daga bakin Avdulmalik makashin Hanifa a lokacin da ake masa tambayoyi, akan yadda aka sassan jikin Hanifa suka bar jikin ta.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.