Labarai

Masu garkuwa da mutane sun budewa motar wasu matafiya wuta a hanyar Tsafe zuwa funtua

Masu garkuwa da mutane sun budewa motar wasu matafiya wuta a hanyar Tsafe zuwa funtua

Shahararran rabubuci Datti Assalafy ya wallafa wani labarin abin tausayi a shafin sa na sada zumunta Facebook kamar haka.

Masu garkuwa da mutane suka fito da babura kan hanyar Tsafe zuwa Funtua a jihar Katsina suka bude wa motar matafiya wuta.

Wannan matar tana rike da yaro karami wanda zaku gani a kwance, harsashin bindiga ya karya mata hannu, sannan harsashin bindigar ya fasa kan yaronta sai da kwakwalwarsa ya zuba, kuma ya mutu nan take, akwai sauran mata a cikin motar bullet ya taba su.

Da zaku kalli hoton yaron nan sai kun zubar da hawaye saboda tausayi, na saka a status dina na WhatsApp, na rufe hoton anan saboda kiyaye dokokin Facebook.

Abin tausayi Kidnappers sun raba uwa da danta, yaro karami da ake shayarwa bai aikata laifin komai, wannan abin ya taba zuciyana sosai Wallahi.

A gaskiya bai kamata Nigeria ta Cigaba da tafiya a haka ba, babu amfanin Gwamnati idan ba za’a iya tsare rayukan talakawa ba, Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari wannan shine abinda yake faruwa a Gwamnatinka.

Mutanen da suke bin hanyar Funtua zuwa Tsafe su kula sosai, jami’an tsaro da suke bin hanyar sunce min na ankarar da mutane, kwanakin nan masu garkuwa da mutane sun addabi hanyar.

Ya Allah Ka kawo mana agaji ba don halin
mu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button