Wani saban al’amari akan Abdulmalik mutumin daya yiwa Hanifa kisan gilla, dafa Datti Assalafy
Datti Assalafy yayi wani bayani akan Abdulmalik mutumin daya kashe Hanifa wanda ya dauki hankulan jama'a
Shahararran marubucin nan Datti Assalafy ya wallafa wata magana a shafin sa na sada zumunta Facebook, inda yake magana akan mutumin daya yiwa Hanifa kisan gilla.
Ga wallafar kamar haka.
Ka nemi halal a gurin Allah, duk wanda ya nema bai samu ba to bai yi hakuri ha, a har kullun masu hakuri su ke da cin nasara.
Duk inda kaga magidanci kamar Abdulmalik da ya hallaka Hanifa ya aikata mummunan laifi irin wannan, to bayan son zuciya da rashin hakuri akwai kuma ingizawar matar aure Abdulmalik wanda yayi garkuwa da Hanifa ya kashe ta.
Yace matarsa ta taimaka masa wajen yin garkuwa da Hanifa domin lokacin da yayi garkuwa da Hanifa gidansa ya fara kaiwa ya boyeta kusan sati biyu da hadin bakin matarsa.
Akwai mutanen da matansu na aure suna basu gudunmawa sosai wajen jefa mazansu na aure ga halaka, wani a kokarin burge matarsa zai jefa rayuwansa zuwa ga halaka da tabewa na har abada.
Duk abinda magidanci zai nema yana nema ne saboda matarsa da ‘ya’yansa, kar ka yadda a gurin neman abinda zaka farantawa matarka rai kaje ka aikata mummunan laifi Ka gane cewa, kana aikata mummunan laifi sai aka kamaka,
Shikenan fa ka rabu da matarka da ‘ya’yanka, matarka zata auri wani yazo gidanka har kan gadon da kake kwana da ita ya Cigaba da kwanciya da ita, idan ya fika lafiyar jima’i cikin lokaci kankani zata manta da kai kana can kana fama a gidan yari kana jiran a zartar maka da hukuncin kisa.
A Kaduna, garin Birnin Gwari, an taba kama wani ma’aikacin gidan biredi da yake kaiwa barayin daji biredi yana sayar musu da tsada, da ake tuhumarsa sai yace neman kudi don ya burge sabuwar amayarsa ya kaishi ga taimakon barayi, gashi yanzu ya rasa matar har abada, wani kato zai aureta yaci gaba da kwanciyar jima’i da ita.
Dan uwa kayi hakuri da matsayin da Allah Yaajiyeka ko iyayen da sukayi sanadin zuwanka
duniya ne suka umarceka ka aikata abinda Allah baya so, to Allah Yace kar ayi musu biyayya a cikin suratu Luqman, balle kuma mata wanda ana iya rabuwa da ita a auri wata Allah Ka karemu, Ka tsare mana imanin mu.