Advertising
Advertising
Labarai

Nomiss Gee wakilin iblis ne duk wanda bai dauki mataki a kai na ba Allah ya tsinewa uban sa, inji Aliyu Imam Indabawa

Wani ficaccan mawaki a kafar sada zumunta mai suna Ali Imam Indabawa ya yi wani rubutu akan mawakin Hip Hop na Arewa24, wanda kuma shine yake jagorantar shirin nan mai suna zafafa 10 wato Nomiss Gee.

Advertising

Ali Imam Indabawa ya yi rubutun ne a shekarar 2020 to a yanzu kuma sai ya sake wallafa wani rubutun tare da yin raddi a cikin sa, wanda hakan yake nuna akwai ‘yar tsama a tsakanin su.

Ga wallafar kamar haka:

An fada din Nomiis Gee wakilin Iblis a doron kasa, wanda ya fasa daukan mataki a kaina Allah ya tsine wa Uban uwarsa, Ba wanda ya fl ni zafin kai da taurin kai, rigima ma da kudi nake siyanta, Allah ya tsine wa wanda ya fasa don ubansa.

Advertising

A yanzu haka za’a iya cewa al’ummar Arewa ba ta da babban kalubale a gabanta ta fuskar tarbiyya da addini sama da wannan shaidanin yaro da a ke kira Nomis Gee.

Da ace mutanenmu na Arewa sun san yadda wannan yaro yake illata rayuwar yaransu ta hanyar lalata musu tunani ya hana su karatu da abin da zai amfani rayuwarsu ya shigar dasu mummunar harkar nan mara amfani ta wake-wake irin na gayun kasashen turawan yamma wacce ke haddasawa matasa shaye-shaye da Zinaceiinace da kazamar harkar nan ta neman maza wa’iyazubillahl.

Da mutanen Arewa sun san barnar da wannan shaidanin yaro yake wa yaransu da tuni sun shiga sun fita sun dauki mataki a kansa, muna da masaniyya yadda wannan yaro yake illata
mana al’umma ta hanyar bin matasa har da ‘kananan yara yana kwadaita musu wannan mummunar harka.

Yana shigo da su ta hanyar haska su a shirin da yake yi gidan Tvn Arewa24, shirin da babu abinda ake nunawa sai badala da alfasha, ta yadda ake nuna mace musulma bahaushiya tayi
mummunar shiga kanta babu dankwali ana ganin saman nonuwanta ga cikinta da cinyoyinta a bude, tana rawar banza ta Allah wadai, ka ga Namiji yayi tatoo yayi ass down shiga ta mashaya masu neman maza.

Tuni mun jima da gane gidan Tvn Arewa24 kwangilar yahudawa ce domin raba al’ummar arewa da addininsu, wallahi hatta wani ma’aikacin gidan ya tabbatar min da haka.

Muna ba wa iyaye shawara da su kula da tarbiyyaryaransu, su kuma daina kunna musu munanan shirye-shiryen wannan tasha, kuma su yi amfani da wannan dama ta wannan wata mai albarka su kai karar wannan mutumi me suna Nomis Gee wajen Allah, har ma gidan arewa24 kamar yadda muke amfani da wannan dama mu yi addu’a a kan bala‘in Coronavirus.

Muna kira ga gwamnatin Kano data baiwa Hukumartace fina—finai cikakken goyon baya domin daukan mataki a kan wannan shaidanin yaro da shirin da yake yi dama tashar baki daya.

Allah ka ci gaba da tonawa Arewa24 asiri tare da sauran makiya addinin musulunci.

lndabawa Aliyu Imam.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button