A Kullum addu’ar da nake Allah ya kawowa matan kannywood mazaje domin suyi aure, cewar Abubakar Bashir mai Shadda
A Kullum addu'ar da nake Allah ya kawowa matan kannywood mazaje domin suyi aure, cewar Abubakar Bashir mai Shadda

A wata shira da aka yi da ficaccan Darakta kuma Furodusa na masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood “Abubakar Bashir mai shadda” ya bayyana cewa, duk wata mace wacce ta taba yin aure ko take da niyyar yi amma take sha’awar shiga harkar to tayi hakuri.
Sannan ya kara da cewa, taje tayi karatu ko kuma ta nemi wata harkar daban idan kuma ta sami miji sai tayi aure yafi mata.
Abubakar bashir mai shadda ya bayyana hakan ne a wata shira da aka yi da shi inda ma a cikin shirar ya kara da cewa.
Yanzu ma harkar fim a cike take suma jarumai mata dukkan su fata nake Allah ya kawo musu mazan aure suyi su tafi dakunan su.
Sannan ya kara da cewa, domin babu abin da yafi dacewa da mace kamar dakin mijin ta, kuma har kullum a cikin basu shawara nake idan sun sami suyi domin shine mutuncin su.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin ku saurari cikekkiyar shirar da aka yi da Abubakar Bashir mai shadda.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.