Tsohon kwamishinan aiyuka Muazu Magaji wani iftila’i ya rutsa da shi a lokacin da ‘yan sanda zasu kama shi
Tsohon kwamishinan aiyuka Muazu Magaji yayi hatsarin mota a lokacin da 'yan sanda zasu kama shi
Muazu Magaji Tsohon Kwamishinan Aiyuka da ya kurumce bayan wani hatsari da ya rutsa da shi lokacin da ‘yan sanda suka biyo shi zasu kama shi a Abuja a jiya Alhamis, kamar yadda lauyansa ya shaidawa Kotun Majistare a jihar Kano.
‘Yan sandan sun kama Muazu Magaji ne bayan yana gudun karya kamu inda yaci karo da fitilar kan titi yana cikin motarsa.
A lokacin da yake yake bayani a gaban Alkalin Kotun “Aminu Gabari” a yau Juma’a Lauyan Magaji “Gazzali Ahmad” yace, wanda yake karewa ya rasa ji na dan wani lokaci sakamakon raunin da ya samu bayan fitar da jakar iska ta yi a motarsa.
Ahmad ya kara da cewa, wanda ake tuhumar ba zai iya sauraron tuhume-tuhumen da ake masa ba balle ya amsa ko akasin haka, domin haka lauyan ya roki kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa domin nemar masa lafiya a asibiti.
A lokacin da yake yanke hukunci kan bukatar lauyan Gabari ya ba da umarnin a kai Muazu Magaji asibitin shalkwatar ‘yan sanda kuma ya cigaba da zama a hannun ‘yan sanda.
Sai dai Gabari ya dage sauraron karar zuwa ranar Litinin 31 ga watan Janairu.