Labaran Kannywood

Wata kotu a jihar kano tasa a kamo mata jarumin kannywood Saddiq Sani Saddiq.

Wata babbar kotu a jihar kano tasa hukumar yan sanda su kano mata Saddiq Sani Saddiq jarumin daya shahara a masana’antar kannywood.

Kotun Shari’a musulunci dake zamanta a hitoro Masallaci ce ta bada wanna sanarwa karkashin me Shari’a Said Adamu ce domin a kamo mata jarumin saka makon ya bijirewa umarnin ta.

Tunda fari dai wani mashiryin Fim wato Aliyu Adamu Hassan ne yakai karar sa sakamakon bashi kudin aiki shirin wasan kwaikwayo shi kuma bai yi aikin ba kuma ake zargin ya hana shi kudin hakan yasa ya garzaya kotun domin rokon ta nemar masa hakkin sa.

Kotun dai ta aike da sammaci amma ba a same shi ba ta kuma bada umarnin a like masa takardar a gidansa da ke Tudun Yola amma har yanzu bai bayyana ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button