Labarai

‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama ciki har da mata masu dauke da juna biyu a jihar Kebbi

'Yan bindiga sun kashe mutane da dama ciki har da mata masu dauke da juna biyu a jihar Kebbi

Rahotanni daga jihar Kebbi dake Arewacin Nageriya sun bayyana cewa, mutane da dama sun rasa rayukan su a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari, cikin wadan da suka rasa rayukan nasu har da wasu mutane da aka bankawa wuta a cikin wani gida.

Bayan da ‘yan bindigar suka kai wani a wani gari a karamar hukumar Ribba ta jihar Kebbi wanda suke makwota da jihar Zamfara a ranar juma’a.

Lamarin tsaro dai a Arewacin Nageriya yaki ci kuma yaki cinyewa wanda abin kara tsamari yake, duk da gwamnatin tarayya tana fadin cewa tana iya bakin kokarin ta na kawo karshen ‘yan ta’addan da suka addabi Arewacin Nageriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button