Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Hafsat Idris ta bayyana farin cikin ta ga masoya da ‘yan uwa kan jaririyar da Diyar ta ta haifa

Jaruma Hafsat Idris ta bayyana farin cikin ta ga masoya da 'yan uwa kan jaririyar da Diyar ta ta haifa

Kamar yadda kuka sani a ‘yan watannin baya da suka gabata an gudanar da auren ‘yar gidan ficaccaiyar jarumar masana’antar kannywood “Hafsat Idris”, inda aka yi shagalin bikin cikin kawatuwa tare da yin dinner ta alfarma.

Advertising

To a yau ne muka sami wata wallafa a shafin sada zumunta na ficacciyar jarumar wato “Hafsat Idris” inda muka ga ta wallafa wata bidiyo dauke da jaririya a hannun wanda ‘yar ta ta haifa.

Jaruma Hafsat Idris tayi murna sosai tare da nuna farin ciki akan jaririyar da ‘yar ta ta haifa wanda har ta sanya wata waka a cikin bidiyon da ta wallafa tana kallon jaririyar tana bin wakar.

Abokanan sana’ar ta kuma jarumai a masana’antar kannywood sun yi murna tare da nuna farin cikin su ga jaririyar da ‘yar ta ta haifa.

Advertising

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domi kuga yadda jaruma Hafsat Idris ta dauki jaririyar tana murna da nuna farin cikin ta a kai.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

https://www.instagram.com/tv/CZJzdK1pcEj/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button