Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Kotu ta bada umarnin kamo jarumin kannywood Sadik Sani Sadik kan zargin sa da ake dayin almundahana

Kotu ta bada umarnin kamo jarumin kannywood Sadik Sani Sadik kan zargin sa da ake dayin almundahana

A yau din nan muka sami wani labari kan cewa, wata kotu dake jihar kano ta bada umarnin kamo ficaccan jarumin masana’antar kannywood Sadik Sani Sadik, kamar yadda Freedomradio ta ruwaito.

Advertising

Wata Kotu a nan Kano ta Umarci ɗan Sandan Kotu daya kamo Mata jarumin wasan kwaikwayon nan Sadik Sani Sadik.

Kotun shari’ar musulunci da ke Zamanta a Hotoro masallaci ƙarƙashin mai shari’a Sagir Adamu ce ta bada umarnin kamo Sadik ɗin sakamakon bijirewa umarnin ta.

Tunda fari dai wani mashiryin Film ne wato Aliyu Adamu Hanas yai ƙarar sa sakamakon bashi kafin alƙalamin kuɗin aiki shirin wasan kwaikwayo shi kuma bai yi aikin ba kuma ake zargin ya hana shi kudin hakan yasa ya garzaya kotun domin roƙon ta nemar masa haƙƙin sa.

Advertising

Kotun dai ta aike da sammaci amma ba a same shi ba ta kuma bada umarnin a liƙe masa takardar a gidansa da ke Tudun Yola amma har yanzu bai bayyana ba.

Wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito cewar me ƙara yana neman Naira dubu tamanin a hannun Sadik ɗin kuma zai sake shigar da ƙara ta neman haƙƙin sa na ɓata masa lokaci da kuma jawo masa asara sakamakon rashin halartar aikin da yayi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button