Labarai

Sadiya Haruna mai kayan mata ta shiga tashin hankali da dimuwa bayan wasu mutane sun sace kanin ta

Sadiya Haruna mai sayar da kayan mata da maza na karin ni’ima ta shiga halin da ya kamata a tausaya mata kuma abi kadun ta, domin a yanzu tana cikin matsananciyar damuwa.

Sadiya Haruna ta wallafa wata bidiyo a shafin ta na sada zumunta instagram hankalin ta a tashe inda take kuka tana fadin cewa, wasu mutane wanda bata san su ba sun je har shagon da take sai da kayan ta sun farmake ta.

Taci gaba da cewa, a lokacin da mutanen suka kai mata farmakin sun kokarin watsa mata asit a sukar ta amma sai Allah ya kare ta, inda nan take ta gudu sai dai kuma sun kama wani kanin ta wanda suke tare a wajan.

A halin yanzu dai Sadiya Hatuna batasan inda mutanen suka kai kanin ta ba abin da ya kara daga mata hankalin kenan, sannan kuma wadan nan mutanen ba jami’an tsaro bane balle taje ta same su domin samin mai ta aikata.

A cikin bidiyon Sadiya Haruna ta roko kan cewa, idan jami’an tsaro ne suka kama kanin ta su sanar da ita inda suke domin ta mika kanta.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin Sadiya Haruna akan abin da ya faru a kan ta da kuma kanin ta, wanda a yanzu haka tana neman agaji akan a dawo mata da kanin ta.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

https://www.instagram.com/tv/CZStNWXq9xe/?utm_medium=copy_link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button