Advertising
Advertising
Labarai

Shugaba Muhammad Buhari ya daba kyautar Mota kirar Golf ga wani mutumi daya taimaka masa a baya

Shugaba Muhammad Buhari ya daba kyautar Mota kirar Golf ga wani mutumi daya taimaka masa a baya

Shugaban kasar Nageriya Muhammad Buhari ya bada kyautar mota kirar Golf tare da kudade har naira dubu dari bakwai (700,000), ga wani bawan Allah mai suna Malam Umar Samll fire.

Advertising

Malam Umar Small fire shine wanda ya dauki Shugaban kasa Muhammad Buhari a motar sa ya kaisa gida yayin da Boko haram suka kai masa hari a kawo kaduna a shekarar 2014.

Shugaban kasar bai iya tunawa da mutumin da ya tseratar da rayuwar tasa ba sai da mutumin ya fito Social Media yayi korafi.

Duk da haka mutane na kallon lallai Malam Umar Small ya taki babban sa’a da ya samu kyautar Mota har da kudi daga shugaban wanda ba’a cika ganin yayi kyauta ba.

Advertising

Ga hotunan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button