Advertising
Advertising
Labarai

Shugaban Kasa Buhari bai dauki rayukan al’ummar Arewa a bakin komai ba da abun da ya iya sai yawon banza, cewar Aisha Yesufu

A wani bidiyo da fitacciyar ‘yar gwagwarmayar nan kuma daya daga cikin wadan da suka samar da kungiyar “BringBackOurGirls” wato Aisha Yesufu.

Advertising

Ta nuna bacin ranta matuka dangane da halin ko in kula da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake nunawa dangane da rayukan al’umma da ake kashewa a kasar musamman ma a Arewacin Najeriya.

Kamar yadda Jaridar Labarunhausa ta ruwaito cewa: Aisha tace ta san ba wai yanzu aka saba zagin ta ba a duk lokacin da ta fito ta caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma a wannan karon dole ta fito tayi magana, inda ta ce, lokacin da tsohon shugaban kasar mulkin farar hula, Shehu Shagari, ya rasu shugaban kasar bai je wajen jana’iza ba.

Aisha Yesufu Ta cigaba da cewa: haka a lokacin da Kanal Abu Ali ya rasu a filin daga, a lokacin da yake kokarin ganin ya kare rayukan al’umma, mutane daga kowanne sassa na kasar nan sunyi gangami don zuwa wajen jana’izar shi, amma shugaban kasar yana Abuja cikin Villa, bai fito ya halarci jana’izar sa ba.

Advertising

Ta kara da cewa: Idan tafiyar banza ce ko taron siyasa a wannan lokacin ne za ka ga shugaban kasar yana rawar jiki, amma duk wani abu da ya shafi talaka babu ruwan shi a ciki, musamman ma idan aka ce a yankin Arewa ne.

Aisha ta:ce: Akwai wani bidiyo da ta taba yi a shekarar 2019, wanda mutane suka yi ta faman zagin ta a kanshi, a lokacin da shubaban kasa yaje jihar Zamfara, ta ce har ya gama ziyarar shi bai yiwa mutanen jihar jaje kan iftila’in da ya afka musu a wancan lokacin ba.

Bayan haka ta kara da cewa: Duka ‘ya’yansa a yanzu babu wani wanda yake da matsala, domin kuwa duka ya riga ya saita su, ya kuma saita kanshi da duka iyalansa, yanzu talaka ne kawai yake shan bakar wahala.

Sannan tace: Aisha ta ce akalla ita a wannan lokacin za ta iya sayen abinci ta ci tayi bacci, amma akwai miliyoyin mutane da babu cin yau babu na gobe, ga bala’in tashin hankali da suke ciki mutane na zaune lafiya lau za a zo a far musu da harbi a kashe na kashewa a yanka na yankawa ayi gaba kuma babu abinda zai faru.

Aisha tace: Ba zai yiwu mutane kawai su zauna su ce iya addu’a kawai za su yi ba domin kuwa ko Annabi Muhammad S.A.W ba a Masallaci kawai ya zauna ba ya fita ya nemawa kanshi da addinin shi hakki a lokacin da ya shiga kunci.

Sabuda ta yi kira ga al’ummar kowacce jiha da su tashi tsaye su fita su gabatar da zanga-zanga domin nunawa duniya da shugabanni cewa abubuwan da ake yi ya isa haka.

Aisha Yesufu ta kara da cewa: Yanzu idan wani ya fito ya fito daga wani yankin na Arewa ya ce yana son shugabancin kasa, da wane baki za su yi magana, domin kuwa a yanzu wanda suka bawa goyon baya, dan Arewa ya gaza yi musu komai, ya bari ana kashe su kamar dabbobi.

Aisha tace: Wannan abu ba wai abu bane na siyasa abu ne da ake maganar rayukan al’umma inda ta bada misali da mutanen da aka kashe a Sokoto a ‘yan kwanakin nan, tace akwai yiwuwar a cikin su akwai wadanda suka dangwalawa shugaban kasar kuri’unsu.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button