Labarai
Yadda wani Matashi ya lakadawa matar Aure duka har takai ya Raunata ta.
Wata Kotu dake zaman ta a Unguwar PRP karamar hukumar Nassarawa a nan cikin birnin jihar Kano ta fara sauraron wata kara ta wani Matashi da ya lakadawa wata matar aure duka har takai ya Raunatata.
Advertising
Matashin ya shiga gidan wani magidanci ne inda ya hadawa matar gidan jikinta har ya lahanta mata ido, wanda yan sandan fararen kaya ne suka gurfanar da wannan matashi a gaban Kotun akan wannan tuhumar da akeyi masa.
Inda aka tura wanda ake zargi zuwa gidan gyaran hali har sai zuwa ranar 11 ga watan biyu na shekarar dubu biyu da ashirin da biyu da muke ciki 11/02/2022 sannan aci gaba da sauraren wannan shari’ar domin girbar abinda ya shuka.
Allah ka kare ya rabamu da biye ma sharrin zuciya
Advertising
Advertising