Advertising
Advertising
Labarai

Asirin wani sojan Nageriya ya tonu bayan an kama shi da laifin fashi da makami shi da wasu ‘yan ta’adda

Asirin wani sojan Nageriya ya tonu bayan an kama shi da laifin fashi da makami shi da wasu 'yan ta'adda

Shahararran marubucin nan Datti Assalafy ya wallafa wani labari a shafin sa na sada zumun ta Facebook, akan wani sojan Nageriya da aka kama mai suna Hassan Abdulhafiz da laifin fashi da makami.

Advertising

Ga labarin kamar haka.

Rundinar ‘yan sandan Nigeria a jihar Yobe
sun kama wani yaro matashin sojan Nigeria
dan shekara 22 mai suna Hassan Abdulhafiz da laifin fashi da makami.

Hassan Abdulhafiz yana aiki da rundinar Army Sector 2 Headquarters karkashin Operation Hadin kai, rundinar da take yaki da Boko Haram a jihar Yobe.

Advertising

Sabida mutuwar zuciya da cin amanar tsaron kasa sai ya hada kai da wasu gurbatattun abokan sa fararen hula Mustapha Abubakar dan shekara 19 da Sama’ila Salmanu dan shekara 25, suka je gidan wata mata mai suna Hajiya Aisha Usman dauke da bindigar AK47 da sauran makamai suka yiwa matar fashi da makami.

Hajiya Aisha tana da zama a unguwar Sabon
Fegi cikin garin Damataru jihar Yobe, bayan sun i||ata Hajiyar da Danta, sun karbi kudi Naira dubu dari biyu da hamsin (250,000), sannan suka tafi da motar Hajiyan kirar Peugeot 307 daga bisani ‘yan sanda suka gano motar a garin Darazo jihar Bauchi sunje zasu sayar aka kamasu.

|rin wadannan maciya amana akwaisu da yawa a aikin tsaro, ba abin mamaki bane idan sun hada kai da ‘yan Boko Haram k0 masu garkuwa da mutane akan kudi, yanzu dai karshen wannan yaron yazo a aikin soja saura ya fuskanci hukunci.

Muna rokon Allah Ya tona asirin duk wani jami’in tsaro da yake cin amanar aikin tsaro a Kasarmu Nigeria.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button