Advertising
Advertising
Labarai

Batan Sadiya Haruna yana da alaka da rigimar su da Teema Makamashi da Isa A Isa, kuma tayi barazanar tona asiri

Batan Sadiya Haruna yana da alaka da rigimar su da Teema Makamashi da Isa A Isa, kuma tayi barazanar tona asiri

Kamar yadda kuka sani tun a shekaran jiya ne Sadiya Haruna mai kayan mata ta wallafa wata bidiyo a shafin ta na sada zumunta istagram, inda take kuka tana fadin cewa wasu mutane sun kai mata hari sannan sun tafi da kanin ta mai suna Umar.

Advertising

Nan da nan bidiyon ta karade kafafun sada zumunta wanda har aka yi ta cece-kuce akan lamarin, bayan haka kuma ake zargin wasu abokanan rigimar ta a kwanakin baya wato Teema Makamashi da kuma Isah A Isah.

To a yanzu ne muka ji wani sautin murya na Sadiya Haruna a ciki wata bidiyo da tashar “Tsakar gida” ta wallafa inda take magana akan rigimar su da Teema Makamashi da kuma dauke kanin ta da aka yi wato Umar a lokacin da wasu mutane suka kai mata farmaki har shagon ta.

A cikin sautin muryar Sadiya Haruna ta fara da cewa, Kun san Sadiya Haruna ko wacece bazan taba wasa da Alkur’ani izu sittin ba ai ba hauka nake ba da zanbi police din kano sau nawa suka nufeni da sharri, ita kan ta Teema Makamashin sau nawa tana karana amma ni nake yin nasara.

Advertising

Sannan Sadiya Haruna bata tsaya nan ba sai ta kara da cewa, ta rantse da Allah za ayi mutuwar kasko ko da wannan abin zai sanadiyyar barin ta duniya to zata fito ta bayyanawa duniya komai tun daga farko har karshe.

Sadiya Haruna tayi bayani sosai a cikin sautin muryar da muka samu a yanzu wanda tashar “Tsakar gida” dake kan manhajar Youtube ta wallafa.

Zaku iya sauraron sautin muryar ta Sadiya Haruna a cikin bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayanin abin da take fada, game da rigimar su da Teema Makamashi da kuma dauke Umar kanin ta da aka yi.

Ga bidiyin nan a kasa domin ku kalla ku saurari sautin muryar Sadiya Haruna.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button