Advertising
Advertising
Labarai

Bayan tayi aure ta haihu ta sami nasarar kammala digirin karatu na Mathematics da first class

Bayan tayi aure ta haihu ta sami nasarar kammala digirin karatu na Mathematics da first class

Wata matar Aure mai suna “Zainab Bello Kofa” ta kammala karatun digirin ta a jami’ar Ahmadu Bello University Zaria, ta karanta Lissafi wanda a turance ake kira da “Mathematics”, ta fito da sakamako mafi daraja a ABU Zaria inda ta samu maki 4.85 -CGPA.

Advertising

Zainab Bello dai matar aure ce kuma tana da yara sai da tayi aure kafin ta fara karatun jami’a, kuma gashi ta zama ta farko a ajin Mathematics.

Don haka karnukan farautar Yehudawa su dena rudar da mu cewa wai aure yana hana karatu, wannan karya ne da makirci ko wace mace zata iya yin karatun ta bayan tayi aure domin hakan zai kara taimaka mata ta wani bangare.

Wasu majiyoyi kuma sun bayyana cewa, wannan baiwar Allah wato Zainab Bello abar ayi koyi da ita ne domin hafiza ce, bayan nasarar data samu a karatun ta na Boko kuma tana da hardar Alkur’ani mai girma.

Advertising

Zainab tun tana yar shekara sha daya 11 a duniya tayi haddar Alkur’ani mai girma wanda idan tabbas gaskiya ne, to ba abin mamaki bane zata iya samun makin karatunta na lissafi fiye da haka duba da daraja da mu’ujizar Alkur’ani mai girma.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button