Labarai
Dan uwan Sadiya Haruna ya bayyana wani al’amari bayan an neme ta sama da kasa an rasa ta
Dan uwan Sadiya Haruna ya bayyana wani al'amari bayan an neme ta sama da kasa an rasa ta
Har yanzu dai ‘yan uwan Sadiya Haruna suna bada sanar wa akan wadan suka dauke ta da su taimaka su dawo da ita, domin a yanzu haka iyayan ta suna cikin damuwa.
Dan uwan nata yake cewa, an abar Sadiya Haruna ta huta kullum tana cikin tashin hankali badan kowa yake hawa instagram ba sai domin ta.
Amma a lokacin da ya hau istagram din yaji labarin an neme ta an rasa wanda hakan ya sanya shi cikin damuwa, inda yace dole ma a hannun jami’an tsaro take kuma da kan su zasu sako ta.
Bayan haka iyayan Sadiya Haruna sun shiga halin damuwa tun lokacin da suka ji labarin an neme ta an rasa.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sauran bayani daga bakin dan uwan nata wanda komai da komai na Sadiya Haruna shi yake rike da su.