Advertising
Advertising
Labarai

Wani Magidanci ya mutu bayan Matar sa ta caccaka masa wuka sabida zai mata kishiya

Kamar yadda kuka sani dai a yanzu Allah ya kawo mu zamanin da matan aure suke kashewa mazajensu, akan abin da bai kai ya kawo ba.

Advertising

To a yau ma mun sami wani labari daga shafin Rariya dake kan dandalin sada zumunta na Facebook, inda suka wallafa labarin cewa wata matar aure ta jashe mijin ta ta hanyar caccaka masa wuka.

Inda suka wallafa labarin kamar haka.

SUBHANALLAH: Matarsa Ta Kashe Shi Ta
Hanyar Caccaka Masa Wuka A Garin
Mararraba Nyaya

Advertising

A daren ranar Asabar ne wani magidanci mai
suna Ibrahim Ahmed (Mai Unguwa) ya gamu
da ajalinsa sakamakon caccaka masa wuka
da matarsa mai suna Atika ta yi.

Lamarin, wanda ya auku a yankin Unguwar
Yerima dake garin Mararrabar Abuja da jihar
Nasarawa, binciken RARIYA ya gano cewa
matar ta yanke wannan danyen hukuncin ne
saboda kara aure da mijin nata ya yi.

Ana sa ran 2a a yi jana’izar mamacin a safiyar
gobe Lahadi, inda ita kuma matar take tsare a
hannun hukuma.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button