Advertising
Advertising
Labarai

Shugaba Muhammad Buhari zai rabawa matasa marasa Digiri Naira 500,000 kowannen su

Shugaban Muhammad Buhari zai rabawa matasa marasa Digiri Naira 500,000 kowannen su

A wani labarin abin farin ciki da muka samu daga shafin Hausaloaded kan cewa, shugaban kasar Nageriya Muhammad Buhari ya bada izinin sakin sama da N14 billion don horas da matasa marasa digiri 500,000 a shirin N-Power na tsawon watanni tara.

Advertising

Hakan ya bayyana ne a zaman majalisar zartarwar tarayya “FEC” da shugaba Muhammad buhari ya jagoranta ranar Laraba 23 ga Maris 2022 a fadar shugaban kasa, Aso Villa.

Ministar jin kai da jin dadin jama’a “Hajiya Sadiya Farouq” ta bayyana hakan ga manema labarai bayan zaman kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sannan Ministar tayi bayanin cewa za’a yi amfani da N14 billion wajen aiki tare da hukumomin gwamnati hudu da zasu baiwa wadannan matasa horo na tsawon watanni tara.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button