Advertising
Advertising
Labarai

Datti Assalafy yayi martani akan fim din da za’a fara haskawa mai suna Hanifa yarinyar da aka kashe ta

Datti Assalafy yayi martani akan fim din da za'a fara haskawa mai suna Hanifa yarinyar da aka kashe ta

Kamar yadda kuka sani a dazu mun kawo muku labarin za’a fara haska wani shirin fim mai dogon zango wanda aka sanya masa suna Hanifa, yarinyar da malamin makarantar su ya mata kisan gilla.

Advertising

To a yanzu kuma mun sami wata wallafa daga shafin sada zumuntar facebook ba ficaccan marubuci Datti Assalafy, inda ya yi magana akan shirin da za’a fara haskawa mai suna Hanifa.

Ga yadda ya wallafa bayanin nasa.

Kungiyar shirya fina-finan Hausa na Arewacin
Nigeria (Kannywood) sun fitar da sanarwa cewa zasu shirya film mai nisan zango (series) akan Hanifa yarinyar da Malaminta na makarantar boko Abdulmalik yayi garkuwa da ita ya kashe ta.

Advertising

Jagoran shirya film din mai suna Ali Sa’id yace a watan biyu zai fara shirya film din Hanifa, yace dalilin shirya film din shine domin ya nuna wa iyaye hanyar da zasu kare ‘ya’yansu, sannan kuma a dinga tunawa da Hanifa, film din mai dogon zango ne, zai fito kashi-kashi.

Ba za’a rasa abin fadakarwa a wannan shirin
film na Hanifa da ake son shiryawa ba, amma
ta wani bangaren yana tattare da illoli da hatsari masu yawa da zai haifar a cikin al’ummah.

|dan masu kokarin shirya film din Hanifa suna son shiryawa ne da kyakkawar niyya na fadakarwa, to su duba abinda zai je ya dawo,
domin kar abinda Abdulmalik ya aikata akan
Hanifa ya zama abin koyi a gurin masu raunin
imani da son zuciya.

Watakila akwai matasa ko yara masu karamar kwakwalwa da suke son su koyi yadda ake garkuwa da mutane amma basu san yadda zasu koya ba, don haka kar film din Hanifa ya zama makaranta na koyar da yadda ake garkuwa da yara kanana har ma da manya.

Masu shirya fina-finai suna bada gudunmawa sosai a duniya wajen koyar da mutane aikata munanan laifuka da zummar cewa wai suna fadakarwa ne.

Akwai fina-finan da suke koyar da dabanci, fashi da makami da sata, lalata da karuwanci, munanan dabi’u da shaye-shaye, rawa da waka, kisan kai, ta’addanci, rashin ladabi da sauran miyagun laifuka da sunan ana wa’azantarwa.

Misali da Kudancin Nigeria, yankin kudu ya tsinci kansa a yawaitar kashe mutane a cire sassan jikinsu don yin tsafi, kuma matasa ke aikatawa, babu inda suka koya face a fina- finan Nollywood na kudancin Nigeria da suke yawan shirya fina-finai akan Money Rituals.

Kuma ko da film din Hanifa ba zai haifar da barna ba, ina ganin abinda aka yiwa Hanifa cin zarafi ne, keta haddi ne da ta’addanci mai taba zuciya da kuma tayar da hankali, bai kamata ya zama abin tunawa ga iyayenta da kuma sauran al’ummah ba.

Muna jawo hankalin hukumar tace fina-finai na jihar Kano ta dauki matakin da ya dace Muna rokon Allah Ya jikan Hanifa, Allah Ya sa ta ceci iyayenta ranar Hisabi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button