Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Masana’antar kannywood zata fara haska fim mai suna Hanifa yarinyar da malamin makarantar su ya mata kisan gilla

Masana'antar kannywood zata fara haska fim mai suna Hanifa yarinyar da malamin makarantar su ya mata kisan gilla

Za’a fara haska wani sabon shirin fim mai dogon zango mai taken Hanifa, yarimyar nan da malamin makarantar su ya mata kisan gilla.

Advertising

Shafin BBC Hausa dake kan dandalin sada zumumta na istagram sun wallafa labarin kamar haka.

Mai Shirya fim din Ali Sa’id yace, a wata mai zuwa ne za’a fara fim mai dogon zango mai taken “Hanifa” kan yarinyar da aka kashe a Kano.

Ali Sa’id yace, babban dalilinsu na yin fim din shi ne domin wayar da kan iyaye kan yadda zasu saka ido kan yaransu bayan abin da ya faru da Hanifa.

Advertising

Muna kuma son a rika tunawa da Hanifa ta hanyar wannan fim din a cewar mai shirya fim din.

lyaye da dama sun nuna sha’awar wannan fim din kuma sun kawo yaransu domin fitowa a matsayin Hanifa a fim din.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button