Labarai
Mawakin hausa Aminu Abubakar Ladan “Alan Waka” ya sake cin sarauta a masarautar Tsibirin Gobir Maradi Niger
Mawakin hausa Aminu Abubakar Ladan "Alan Waka" ya sake cin sarauta a masanarautar Tsibirin Gobir Maradi Niger

Fitaccen mawakin hausa Aminu Abubakar Ladan wanda aka fi sanin sa da Alan waka, ya sake samun wata sabuwa sarauta a nahiyar tsibirin maradi niger kamar yadda jaridar Gobirmob ta ruwaito.
Fadar Maimartaba Sultan Abdul Bala Marafa “Magajin Bawa Jangwarzo” ta fitar da sanarwar nadin sarautar fitaccen mawakin Hausa Alan Waka, wadda za’a yi a garin Tsibirin Gobir Maradi Niger.
Za’a yi Alan Waka sarautar ne a ranar 13 ga watan Fabrairu kamar yanda sakon katin gayyata ya kumsa, A shekarun baya Alan Waka yaci sarautar Danburan Gobir a masarautar Gobir ta Sabon Birni dake jihar Sokoto.