Sheikh Murtala Bello Asada ya sake tonawa gwamnan jihar zamfara asiri bayan ya saki wani dan ta’adda
Sheikh Murtala Bello Asada ya sake tonawa gwamnan jihar zamfara asiri bayan ya saki wani dan ta'adda
Ficaccan marubucin nan Datti Assalafy ya wallafa wani labari a shafin sa na sada zumunta Facebook, akan tonon asirin da Sheikh Murtala Bello Asada Sokoto ya yi ga gwamnan jihar Zamfara.
Ga wallafar kamar haka.
Sheikh murtala Bello Asada Sokoto ya sake tonawa Gwamnatin jihar Zamfara asiri bayan
ta saki wani babban ‘dan ta’adda Abubakar
Kamarawa abokin Musa Kamarawa wanda
yake kaiwa su Bello Turji takalma da kakin sojoji.
Malam Murtala yayi tonon asirin maciya amanar tsaro inda malam ya kalubalanci Gwamnatin Sokoto da Zamfara cewa, duk wani jami’in Gwamnati wanda ya haihu a cikin mahaifiyarsa ya kaishi kotu idan sharri yake musu.
Muna rokon Allah Ya tsare malam Murtala Bello, Allah Ya tonawa duk wani maciyin amana asiri, Allah Ka kwace mulki daga hannunsu.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin ku saurari cikekken bayani daga bakin malamin.