Wani kirista ya shiga addinin musulinci sabida yawan kallon shirin izzar so na tashar Bakori Tv
Wani kirista ya shiga addinin musulinci sabida yawan kallon shirin izzar so na tashar Bakori Tv
Wani kirista dan asalin jihar Cross River karamar hukumar Idom Ikon mai suna John ya rungumi addinin musulinci hannu biyu-biyu inda yace, hakan ya faru ne sabida tsabagen kallon shirin nan mai dogon zango na Izzar so da yake yawan yi ako da yaushe.
Hakika wannan babban al’amari ne sabida John ya karbi addinin musulinci ba ta ko wace hanya ba, sai ta hanyar kallon shirin hausa na Izzar so mai dogon zango.
John dai yayi tattaki tun daga jihar Cross River har zuwa jihar kano inda mashiryin shirin na izzar so yake wato Lawan Ahmad, kuma shine yake taka rawa a cikin shirin da suna Umar Hashim.
Hakika Lawan Ahmad ya yi matukar farin ciki da wannan al’amari kasancewar mutum yabar addinin sa na kiristanci zuwa addinin musulinci sabida kallon fim din sa na izzar so.
Lawan Ahmad da kan sa ya wallafa wannan abin farin cikin a shafin sa na sada zumunta istagram, inda ya wallafa wani rubutu kamar haka.
Masha Allah a yau ne mukayi wani babban kamu a musulinci inda wannan bawan Allah ya shiga musulinci sabida kallon izzar so da yake yi, tun daga Cross River Udom Ikon Lokal goevrnment Cross River.
Yanzu haka dai ya karbi musulici kuma yanzu haka sunan sa ya koma Umar daga John, muna yi masa addu’ar Allah ya sa ya shigo addinin musulinci a sa’a Allah ya sa ya amfaneshi, Ameen.
Bayan Lawan Ahmad ya yi wannan wallafar mutane da dama sun bayyana farin cikin su akan lamarin, inda aka yi ta yiwa wanda ya musulinta addu’o’in fatan alkairi.
To zamu iya cewa dai ba wannan ne karo na farko da kiritoci suke musulinta sabida kallon fina-finan hausa ba, duk da cewa har yamzu yawancin malaman addini suna Allah wadai da fina-finan.
Yanzu dai ga bidiyon yanda lamarin musulintar mutumin ya kasance, kamar yadda muka dauko daga shafin sada zumuntar istagram na Lawan Ahmad, wato Umar Hashim a cikin shirin izzar so.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.