Advertising
Advertising
Labarai

Wata musulma ‘yar wasan kwallon hannu taki buga babban wasa dalilin an bukaci ta tallata kungiyar Madigo da Luwadi

Wata musulma 'yar wasan kwallon hannu taki buga babban wasa dalilin an bukaci ta tallata kungiyar Madigo da Luwadi

Musulma ta farko mai kishin addinin ta wacce aka fara samu a kungiyar kwallon hannu ta “AFLW” zata kauracewa cigaba da buga wasa a wannan shekara, sabida tsananin kishin addinin Musulunci da take yi.

Advertising

Tauraruwar ta kulub din “Western Sydney Giants” mai suna Haneen Zreika, ta kauracewa shiga zagayen wasan na wannan mako sakamakon kin sanya riga mai nuni da goyon bayan LGBTQI ta kungiyar ‘yan luwadi da madigo , sabida ta yarda da cewa addininta ya haramta goyon bayan irin wannan kungiya.

Kamar yadda Labarun hausa suka ruwauto ruwaito cewa, budurwar ‘yar shekara 22 ta shaidawa ‘yan kungiyar wasan nasu ne dangane da matsayarta, inda kuma suka gamsu kuma suka mara mata baya.

Bayan haka anyi kiyasin cewa, kimanin kashi 75 zuwa kashi 80 na gasar kungiyar “AFLW” duk na kungiyar LGBTQI dinne.

Advertising

Budurwar mai suna Haneen Zreika ta buga wasan da kungiyar ta “AFLW” a shekarar 2021 da ta gabata, inda akayi wasanni kala-kala da kuma magoya bayan bangarori da yawa, amma ‘yan kungiyar tasu basu sanya rigar ta LGBTQI mai dauke da alamar ‘yan luwadi da madigon ba.

Amma wasu daga cikin ‘yan wasan na “AFLW” da suka amince suka sanya rigunan LGBTQI wanda ke dauke da alamar ‘yan Luwadi da Madigo ga hotunan su a kasa.

‘Yar wasan kwallon hannun mai shekara 22 ta ci kyautar kwallon shekara a kakar gasa ta shekarar da ta gabata. Sannan ta wakilci Giant din a babbar gasar gudun zangon karshe.

Shugaban zauren majalisar Malaman addinin Musulunci na Victoria ya gayawa The Age cewa, abune mai mahimmanci da ta kauracewa wasan indai tayi hakan ne domin tana ganin hakan ya sabawa addinin ta.

Abu ne mai tsauri. KasantuwarAFL yankine na hadakar mazauna, amma akwai girmama mabanbatan ra’ayoyi. Ina fata, kuma itama na
tabbata tana fatan hakan, cewa da kungiyar wasan da kuma yan yankin AFL, duk zasu martaba matsayarta.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button