Labarai

An bada cikiyar wasu ‘yam mata wanda suke neman lalata rayuwar su ta hanyar shiga harkar fim

An bada cikiyar wasu 'yam mata wanda suke neman lalata rayuwar su ta hanyar shiga harkar fim

An bada sanarwar gaggawa akan wasu ‘yam mata guda biyu masu suna Fiddausi da Hauwa’u wadanda suka bazama neman shiga shirin fina-finai na masana’antar kannywood.

Alamomi dai sun nuna cewa ‘yam matan sun bijirewa iyayan su ne inda suka futo daga gidajen su suna neman wanda zai taimaka ya sasu a harkar fim.

Sai dai akwai wata doka a hukumar tace fina-finai wacce take cewa, babu wata jaruma da za’a saka a fim har sai da amincewa da sa hannun iyayan ta ko kuma masu kula da ita.

Domin kuwa ta haka ne wasu bata gari suke amfani da damar su wajan yin zinace-zinace da ‘yayan mutane, wanda hakan kowa yasan ba karamin laifi bane a wajan Allah, domin kuwa Allah ya fada a Qur’ani cewa kada a kusanci zina balle ma har a aikata ta.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sanarwar da aka yi akan wadannan ‘yam matan guda biyu, wanda suke neman shiga harkar fim ba tare da sanin iyayan su ba.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button