Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Banga wani sammaci daga kotu ba kan karar da ake cewa an shigar da ni, cewar Sadiq Sani Sadiq

Banga wani sammaci daga kotu ba kan karar da ake cewa an shigar da ni, cewar Sadiq Sani Sadiq

Kamar yadda kuka sani a ‘yan kwanakin nan ne wata kotu a jihar kano take neman jarumin kannywood Sadiq Sani Sadiq, kan yin almundahana da wasu kudade da aka bashi domin yin wani aikin shirin fim.

Advertising

Wanda har aka tura jami’an tsaro domin su kamo shi amma ba’a same shi inda kotun ta daba umarnin a lika masa takardar tuhumar da ake masa a gidan sa.

To a yau kuma Jarumi sadiq sani sadiq ya tattaunawarsu da gidan jaridar murya amurka wato voahausa, inda suka yi hira da shi akan kudin wani furodusa da yaci wanda har kotu take neman sa amma ba’a same shi ba.

Aliyu muhammad hanas ne wanda ya bashi kudi kimanin naira dubu dari 100k wanda kaso ne daga cikin kason aikin da zaiyi wanda jarumin yace yanzu kusan shekara biyar kenan.

Advertising

A lokacin da Jarumi sadiq sani sadiq yake shira da jaridar voahausa ya bayyana cewa, shi bai ga sammaci ba kuma baiga wata takarda daga kotu ba wanda take nuna ana nemansa.

A cikin shirar zakuji bayyani tiryan tiryan daga bakin jarumin Sadiq Sani Sadiq domin hausawa suna cewa, waka a bakin mai ita ta fi dadi.

Ga shirar ta su nan da gidan jaridar voahausa domin ku saurara.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button