Labaran Kannywood

Malam Ali na Kwana Casa’in 90 ya bada labarin abin da jarumi Ali Nuhu ya yiwa wata yarinyar mai tallar awara

Malam Ali na Kwana Casa'in 90 ya bada labarin abin da jarumi Ali Nuhu ya yiwa wata yarinyar mai tallar awara

Jarumi Abdul Sashir wanda aka fi sani da malam ali na cikin shirin dadin kwana casa’in 90 mai dogon zango, ya bada labarin yadda wani abokin sa ya yabi Sarki Ali Nuhu wajen aikata alheri, yadda Ali Nuhu ya dauki kudin aikin sa kacokan ya bawa wata yarinya mai talla datayi barin awarar ta, Tun daga lokacin abokin nasa yace yake jinjinawa Ali Nuhu ga yake masa kallon mutumin kirki ne.

Ga wallafa da Abdul Sashir ya yi akan mutumin da yabi Ali Nuhu.

Jiya nake Hira da wani abokina sai yake cemin Abdul walh Ali Nuhu yatabayin wani Abu Wanda yatabani,nake tambayarshi mene yafaru? Sai yace watarana yaga wata yarinya Mai tallan awara tana kuka alamar tayi barin awararta. Saiga Ali Nuhu yafito Yana zuwa yaga yarinyar tanata sharbar kuka.

Nan take yaje har inda yarinyar take yatsaya yake tambayarta shin mene yake faruwa dake? Saitace awaratace ta bare sai yace to daina kuka kinji ya dauki kudi masu kauri yace ga wannan rike nabaki duka kije Ammafa kidaina kuka.

Bayan Ali Nuhu yashiga mota yatafi sai mutanan wajan sukace wannan kudinda Daya bawa wannan yarinyar fa yanzu yayi aikin wani voice over aka bashi kudin, ko Aljihu Bai saka kudinba ya dauka yabawa wannan yarinyar.

Abokina yace shifa tundaga Nan ya sallamawa Ali Nuhu akan gaskiya Wannan mutumin kirkine.

Muna alfahari dakai matuka sir @realalinuhu this is the full definition of humanity.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button