Shugaba Muhammad Buhari yayi bayani akan juyin mulkin da za’a daina yi a kasar Nageriya
Shugaban kasar Nageriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa, baza’a sake yin wani juyin mulki na sojoji a Nageriya ba.
Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a lokacin wani martani kan damuwar da gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya nuna, kan guguwar juyin mulki da ta taso a Afirka da ta hada da hambare gwamnatocin domokradiyya a Mali, Guinea da Burkina Faso.
Kamar yadda Kamfamin Daillancin Labarai na kasa “NAN” ya rawaito cewa, Buhari ya bayyana cewa, yana da yakinin cewa Nijeriya ta wuce lokacin yin juyin mulki.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata liyafa da kwamitin ‘yan siyasa da ƴan kasuwa tare da ‘yn jarida da kungiyoyi masu zaman kansu suka hada a fadar shugaba kasa a jiya Litinin.
Sannan kuma a watan Nuwambar 2021 ne Buhari tsohon shugaban kasa na mulkin soji ya jaddada cewa, Afirka baza ta lamunci juyin mulki ba bayan da aka yi juyin mulki a Guinea da Mali.