Yadda aka gudanar da shagalin bikin sunan jikar Hafsat Idris
Kamar yadda kuka sani Diyar ficacciyar jarumar masana’antar kanywood Hafsat Idris ta haihu wanda har aka saka sunan Hafsat Idris din, wanda har ta wallafa wata bidiyo a shafin ta na instagram tana bayyana farin cikin ta kan jaririyar da Diyar ta ta haifa musu.
To a yanzu kuma mun sami wata bidiyo daga tashar Tsakar gida dake kan manhajar Youtube inda muka ga jaruma Hafsat Idris tare da abokan sana’ar ra da kuma ‘yan uwan ta suna bikin nuna murna ga jaririyar da Diyar ta ta haifa.
A hausance dai ana kiran wannan shagalin bikin da “Suna” wato a randa za’a sakawa jariri ko jaririya suna, to a ranar akan gudanar da wannan shagalin bikin.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga yadda aka gudanar da shagalin bikin sunan jaririyar da Diyar Hafsat Idris ta haifa.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.