Advertising
Advertising
Labarai

Anyi kira ga hukumar hisbah data kama matashin da yake sa ‘yam mata suna masa kiss a bainar jama’a

Anyi kira ga hukumar hisbah data kama matashin da yake sa 'yam mata suna masa kiss a bainar jama'a

Wani matashi mai suna Ahmad wanda yake yawo wuraren taron jama’a a cikin garin kano yana wani abu da ya kasance kamar al’ada ce ta turawa a kafafan sada zumunta, inda za’a yiwa mutum tambayoyi ko a bashi zafi wanda mafi aka sari akan samu na abin dariya ko abin al’aja bi daga mabanbantan mutane.

Advertising

Matashin ya fara wannan abu da harshen hausa da kuma hausawa musamman ‘yam mata ko masoya inda yafi zuwa babbar kasuwar zamanin nan ta Ado Bayero Mall, sai dai matashin ya fara bata rawar sa tsalle bayan da ya fara yiwa ‘yam mata tambaya a cikin kiss ko mari wanne zasu zaba, inda kananan yaran ‘yam matan hausawa suke masa kiss a bainar jama’a ko su masa marin wasa.

Mufeeda Rashid ta wallafa bidiyon wasannin da yake a shafin ta na instagram gami da jan hankali kan lamarin matashin inda tayi rubutu kamar haka.

Ga wani matashi Musulmi Bahaushe mai kitso a
kanshi da gashi, yana yawan zuwa Ado Bayero Mall Kano yana tare ‘yan matan mutane da suka je sayayya yana yin hira da su, sannan yaje ya daura a shafinsa na Tiktok.

Advertising

Kamar yadda zaku gani a wannan bidiyon, abinda matashin yake yi kenan, sai ya sa budurwa ta zabi ya mata kiss ko mari bayan ya gama hira da su, kamar yadda yasa wannan yarinya ta masa kiss, daga nan sai yaje ya daura a shafinsa na Tiktok.

Wannan dabi’ar a kasashen Yahudawa ake yinta, yau mun wayi gari ga wani ‘dan Musulmai ya kawo dabi’ar garin Kano.

Muna kira ga rundinar Musulunci Hisbah reshenjihar Kano ta gaggauta daukar matakin da ya dace domin bai fl karfin doka ba.

Muna rokon Allah Ya karemu daga sharrin fitinar
karshen zamani.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button