Fati Slow ta karyata zargin da Sadiya Haruna take yiwa jaruma Teema Makamashi
Har yanzu dai ana cigaba da tattauna magana akan rigimar da taki ci taki cinye wa tsakanin Sadiya Haruna da jarumar kannywood Teema makamashi, wanda a yanzu rigimar ta sake dawowa danya bayan wani kanin Sadiya Haruna da aka sace mai suna besty.
Idan baku manta ba a jiya ne muka kawo muku labarin yadda Sadiya Haruna take bayyana cewa, zata yi karar mutane da suke addabar rayuwar ta inda har muka sanya muku wata sautin muryar ta wanda take bayyana hakan a ciki.
To a yau kuma mun sami wata bidiyo wanda Fato Slow wanda ita ma jaruma ce a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood, inda take karyata Sadiya Haruna kan zargin da take yiwa Teema makamashi.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji bayani daga bakin Fati Slow akan karyata Sadiya Haruna da tayi game da zargin da take yiwa jaruma Teema makamashi.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.