Advertising
Advertising
Labarai

Jami’an tsaro sun kama likitan dan ta’adda Bello Turji tare da wasu yaran sa

Rundunar ‘yan Sanda a jihar Sokoto ta kama wani likita dan ta’adda Bello Turji mai suna Abubakar Hashimu, wanda yake kula da kasurgumin jagoran ‘yan fashin dajin nan mai suna Bello Turji lokacin da sojoji su ka ji masa raunuka a wani hari da su ka kai masa shekaru 3 da su ka wuce.

Advertising

A lokacin da yake ganawa da manema labarai a a jihar Sokoto a ranar Litinin “Ahmed Zaki” Mataimakin Sifeto Janar na bangaren aiyuka ya bayyana cewa, an kama Hashim ne tare da wasu mutane talatin da shida 36.

Wasu daga cikin yaran Bello Turji da aka kama sun hada da ,Musa Kamarawa, Bammi Kiruwa, Zayyanu Abdullahi, Hardo Yunusa da Samuel Chinedu da dai sauran su.

Kamar yadda Ahmed Zaki yace, an yi kamen ne tsakanin 20 ga watan Janairu da 29 ga Janairu inda ya kara da cewa, ‘yan sandan Operation Sahara Storm sune suka kama ‘yan ta’addan bayan da suka kai sumame a illela, Rabah, Isa da karamar Hukumar Goronyo a Jihar Sokoto.

Advertising

Sannan ya kara da cewa, bayan sumamen an kama mutane talatin da bakwai 37 tare da kayan laifi da dama a wajen su.

A cewar Ahmed Zaki, dukkan su suna da alaka da Bello Turji kuma sun amsa cewa, suna da hannu a ta’addancin fashin daji da ake yi.

A karshe Ahmed Zaki yace, ana ta bincike a kan lamarin inda ya kara da cewa ana kammala binciken za’a gurfanar da su a gaban kotu domin su girbe abinda su ka shuka.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button