Advertising
Advertising
Labarai

An bayyana rashin fa’idar dake tattare ga Macen daba Matar aure ba tana sanya Hoda kuma ta fita Maza su ganta

Da dai farko a Mazhabar Shafi’iyya da Malikiyya, da Hanabila gaba dayansu sun tafi kan cewa fuskar mace al’aura ce kuma dole ne ta rufe fuskarta wajibi ne, bude fuska haramun ne.

Advertising

Albany ya kawo wannan maganar a littafin sa Jilbab cewa, wajibine macae ta rufe fuskarta, haka ma mai littafen Tarbiyatul Aulad Nasihil Ulwan shima yakawo wannan maganar.

Mazhabar Hanafiyya ce kawai suka ce fuskar mace ba dole ba ne ta rufe fuskarta ya halasta ta bude fuskarta In dai ba’a tunanin fadawa cikin fitina, sannan idan an tabbatar ana lokacin aminci to ba komai tana iya bude fuskar ta.

Imam Ibn Katheer ya fada cewa, bai halatta ba ga macace ta bayyana fuskarta ba sai a waja muharramin ta (Tafsir Ibn Katheer 3/274).

Advertising

Haka An tambayi manyan Malamai masu bayarda Fatawa a Saudiya cewa, koo Macace zata Iya yin Kwalliya?, sai suka bada amsa da cewa, hakika babu abinda zai hana macace yin kwalliya sai dai kuma bai halatta ga macace tayi kwalliya ga wasu mazan wayanda ba muharramant ba, (Fataawa Al-lajnah al-Daa’imah (17/129).

Dukkan Malaman Sunna sun fadi cewa, bai halatta ga macace marar aure ta yi kwalliya ba (musamman da abinda zai canja mata fatar jiki), domin idan wani namiji ya ganta yana sonta da aure zai yi tunanin fara ce, ta dalilin wannan hodar da ta sanya wanda kuwa a aure ba’a bukatar boye kama.

Haka kuma matar aure zata iya yin kwalliya amma idan daga ita sai ‘yan uwanta mata ne a gidan ko kuma muharraminta, (Miji, Kanenta ko ‘yayan ta, Mahaifinta, Mahaifin mijinta dasauransu).

Haka kuma a cikin Fatawar Al-lajnah al-Daa’imah sun bayyana cewa, Matar aure zata iya yin kwalliya makawar babu wanda zai ganta, amma idan wanda ba muharraminta ba ya ganta to ana kwautata zaton za’a iya rubuta mata zunubin fita “Tabarruj, bama yin kwalliya ta fita ba bude fuskarta ma ta fita wasu malumma suna ganin kuskurene.

Shiekh Usaimin yace, fuskar mace nan ne matattarar fitina kuma nan ne wurin farko da mace zata rufe kuma mutane da dama suna sakaci wajen barin yaran su na fita fuskar su a bude wanda bai kamata ba. (Usratul muslima).

Shima sheikh Muhammad bn AbdulMaqsud yana da fahimtar mace ta rufe dukkan jikinta baki daya kar ta bar komai sai dai idonta da za ta ga hanya, hujar sa hadisin bn Mas`ud wanda Imamu Tirmidhi yaruwaito da isnadi igantacce. “Mace al`aurace mu kuma an umurce mu da mu rufe al`aura” (Fatawaa Mar`atul Muslimah 602).

A karshe Ina cewa, Mai son ganin bayani sosai sai ya duba littafin Imamul Kurdubi ko Tafsirin Baydawi ko ibn Kasir ko Mahasinu Tanzil ko ka duba Jilbabul mar atil muslimah na Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albany ko Audatul hijab da Libasul Yaum na Ammru da Sarimul mashur alt Tabarurj.

Jamilu Sani Rarah jihar Sokoto
Thu 03-02-2022
.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button