Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin kasar Nageriya ta tono wasu mutane da suke daukar nauyin ‘yan Boko Haram da ISWAP

Gwamnatin kasar Nijeriya ta bayyana cewa, ta bankado wasu mutane masu daukar nauyin ta’addanci a kasar har guda casa’in da shida 96, musamman ma wadanda suke goyon bayan Boko Haram da ISWAP.

Advertising

Ministan yada labarai na kasa Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a kan irin nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu na yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Sannan yace a nata bangaren a nazarin da Hukumar Hada-hadar Kudi ta Sirri ta kasa “NFIU” a 2020-2021, ta bankado mutanen da suke daukar nauyin ta’addanci a Nijeriya.

Bokan da ake harkar da shi na masu daukar nauyin ta’addanci su 424 da sa hannun wajen kamfanunuwa 123, da kuma kamfanonin canjin kuɗi 33 gami da bayyana ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane 26 da kuma masu taimaka musu guda 7.

Advertising

Nazarin ya haifar da kama mutane arba’in da biyar 45 da kwanan nan za a yanke musu hukuncin a kotu da kuma kwace kadarorin su.

Mame da daukar nauyin ta’addanci “NFIU” na musayar bayanan sirri da kasashe goma sha tara 19 a kan Boko Haram, ISWAP, fashin daji da garkuwa da mutane.

Da ga lokacin 2020-2021 “NFIU” ta maida kudaden damfara da su ka kai dala 103,722,102.83, 3,000, fam 7,695 da kuma dalar singapore 1,091 ga ƙasashe 11.

Advertising

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button