Jerin kananan yaran da aka yi garkuwa da su sannan aka musu kisan gilla a Arewacin Nageriya
Kamar yadda kuka sani a kwanan nan da muke cike ake ta yada labarai daban-daban a kafafan sada zumun ta, inda ake ta kashe kananan yara wanda basu ji basu gani ba ta hanyar yin garkuwa da su.
Wanda a kalla an kashe kananan yara sun kai biyar duk kusan lokaci guda, wanda abin ya kara tayar wa da al’umma hankali.
To a yau ne tashar “Gaskiya24 Tv” dake kan manhajar Youtube ta kawo jerin kananan yaran da aka yi garkuwa da su sannan aka kashe su.
Kamar yadda suka jero yaran da aka kashe da kuma bayanin su kamar haka.
Yarinya ta farko ita ce Husnah: Ana tsaka da jimamin kisan gillar da aka yiwa karamar yarinyar nan Hanifa sai kuma wani labarin ya bulla na kashe wata karamar yarin mai shekara takwas a Zariya dake jihar Kaduna.
Wanda a lokacin BBC ta tuntubi mahaifin Husnah Alhaji Wa’alamh Uban Dawaki inda ya tabbatar musu da cewa, an sace ‘yar sa ne tun a karshen shekarar data gabata kuma ta shafe kwanaki arba’in da daya tana hannun wadanda suka sace ta.
Sannan kuma a watan Yulin shekara ta 2019 an sace wata karamar yarinya mai suna Aisha Sani a unguwar Tudunwada dake cikin birnin jihar Kano, inda aka yi zargin wata mata ce ta sace ta bayan taso daga makaranya zata koma gida Bayan mako biyu da sace Aisha sai aka tsinci gawar ta.
Sai kuma kisan Hanifa mai shekaru biyar a garin Kano: Kisan Hanifa shine na baya’baya nan wanda ya dagawa al’umma hankali sosai a shafukan sada zumun, dama wadanda basa amfani da shafukan.
An sace Hanifa tun ranar 4 ga watan Disamba 2021 a kan hanyar ta ta komawa gida bayan ta taso daga makarantar Islamiyya, inda rahotanni suka tabbatar da cewa wasu mutane ne suka dauke ta a babur mai kafa uku wato adaidaita sahu inda aka yi ta neman ta aka rasa.
Sai wani karamin yaro mai suna Al’amin Adamu mai shekara 4: A shekarar 2019 wani yaro ya bata a garin Patiskum dake jihar Yobe daga baya kuma sai abin ya zama ashe ba bata yaron ya yi ba masu garkuwa da mutane ne suka sace shi, daga karshe an kama wadanda suka yi garkuwa da yaron amma sai dai sun kashe shi.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa wanda tashar “Gaskiya24 Tv” ta jero kananan yaran da aka yi garkuwa da kuma aka musu kisan gilla, domin kuji karashen bayani.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.