Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Nan bada jimawa ba zan yi wuff dake abar kauna ta, cewar Lilin Baba masoyin Ummi Rahab

Nan bada jimawa ba zan yi wuff dake abar kauna ta, cewar Lilin Baba masoyin Ummi Rahab

Kamar yadda kuka sani a yanzu haka dai ana tsaka da soyayya tsakanin jarumar kannywood Ummi Rahab da kuma mawaki Lilin Baba.

Advertising

A wannan makon ne mawaki Lilin Baba ya taya masoyiyar tasa Ummi Rahab murnar zagayowar ranar haihuwar ta, inda har ya wallafa wasu kalaman a shafin sa na sada zumunta isntagram tare bayyana cewa ya kusa yin wuff da ita.

Soyayyar tasu dai har yanzu kara karfi take wanda ana ganin nan daba jimawa ba zasu iya aurar junan su, duba da wata wallafa da Lilin Baba ya yi a shafin sa na sada zumun kan masoyiyar tasa Ummi Rahab.

Mawaki Lilin Baba ya wallafa kalaman soyayya a shafin nasa na instagram masu ratsa zuciya akan masoyiyar tasa Ummi Rahab, a lokacin da yake taya ta murnar zagayowar ranar haihuwar ta wanda a turance ake kira da “Happy Birthday”.

Advertising

Inda ya wallafa hoton Ummi Rahab tare da rubutu kalaman nasa a kasan hoton kamar haka.

Barka da zagayowar ranar haihuwa abar kaunar rayuwata @ummirahabofficial. Hakika ke ta daban ce mai zuciyar zinari. “Ina aika sakon zagayowar ranar haihuwa ta musamman gare ki yayin da kika kara shekara daya a yau! Ina fatan kin cika da farin ciki da annashuwa a yau. Abun farin ciki ne ganin irin matar da kika zama a yau. #HappyBirthday UMMI. “Ina miki fatan alkhairi a duniya da lahira, Allah ya ci gaba da sanya albarka a rayuwarki. Karin nasara a gare ki . NA KUSA NA YI WUFF DA KE IN SHAA ALLAH.

https://www.instagram.com/p/CZeO84Lo6_T/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button