Advertising
Advertising
Labarai

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da shirin rage haihuwa a Nageriya

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da shirin rage haihuwa a Nageriya

Shahararran marubucin nan Datti Assalafy ya wallafa wani labari a shafin sa na sada zumun ta Facebook kamar haka.

Advertising

Kamar yadda na ga wannan labarin a BBC, Shugaban Muhammadu Buhari ya kaddamar
da shirin rage haihuwa a Nigeria.

Buhari yace akwai bukatar daukar matakan
gaggawa domin shawo kan karuwar da ake samu na haihuwa ta hanyar fadada shirye shiryen samar da hanyoyin bayar da tazarar
haihuwa na zamani a fadin Kasar.

Na tabbata shugaba Buhari a karan kansa ba zai rikitowa kansa wannan masifa na hana haihuwa ha a lokacin da yake kara fuskantar kabari, makircin makiya ne wannan.

Advertising

Duk duniya ba’a haifi uwar wanda zai 20 ya hanamu haihuwa ba, zamu Cigaba da raya Sunnah da matan mu na Aure, ku ji da kyau
wakilan Yehudawa, zamu Cigaba da yiwa
matanmu ciki suyi ta haihuwa kamar yadda
kowa aka samu cikinsa aka haifo shi yazo duniya.

Mukarraban Buhari da kuka kawo masa wannan ajanda ta Yahudawa, kun manta cewa albarkacin yawan haihuwa kukaci, haifaffu a cikin iyayensu suka zabeku kuka kafa Gwamnatin da kuke cin moriyarta daga ku sai ‘ya’yanku da matanku da kawalanku, zabar Gwamnatin ku da akayi laifi ne?.

Kuma me yasa bakwa kawo tsarin daukar mataki akan kaaruwai da suke yin cikin sheegee suna haifan ‘ya’yan da ba na halal ba?.

Ina ganin bai kamata ku dauki mataki akan abinda Allah Ya halatta ba kuma yake bayarwa ba.

Allah ne Ya ke bada haihuwa, duk wanda yace zai hana to ya nemo wa kansa fada da Allah, lokacin da Allah zai halicci mutum a cikin mahaifa baya shawara da kowa, Allah yake bada haihuwa kuma yake hanawa a lokacin da Ya ga dama.

Ba zamu taba yadda da duk wani wakilin Yahudawa ba, duk wanda zai kawo mana tsarin hana haihuwa Wallahi ba zamu yadda da shi ba sai ya kawo tsarin hana cikin sheegee.

Muna fatan Allah Ya fahimtar da shugaba Buhari shirin Yehudawa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button