Labarai

Duk iskancin da ‘yam matan TikTok suke aikatawa amma haka ake aurar su a kyale mu masu Hijabi, cewar Arewa Queen

Duk iskancin da 'yam matan TikTok suke aikatawa amma haka ake aurar su a kyale mu masu Hijabi, cewar Arewa Queen

Kamar yadda kuka sani dai akwai ‘yam matan hausawa wanda suke sheke ayarsu a dandalin TikTok, inda suke wallafa bidiyoyin da suke bayyana surar jikin su sannan kuma suna rawa.

Wata matashiyar budurwa mai suna “Queen” ta fadi ra’ayinta game da ‘yam matan TikTok kan abubuwan da suke aikatawa, amma duk da haka sai kaga ana aurar su ba’a aurar matan da suke mutunta kan su.

Queen ta fara da cewa: Gaskiya ana yada badala a dandalin Tiktok sai kaga yarinya bahaushiya ta saka Bum short ko mini skirt da crop top cibiyar ta a waje tana rausaya da kada jiki.

Sannan kuma duk da iskancin nan ba zai hana kaga an zagaya ana aurar su ba mu a bar mu da Hijabi tunda iyayen su suna da ‘iyayan banki.

Queen dai ‘yar jihar Kaduna ce wacce take zaune ce a birnin birnin zazzau, ta bayyana hakan ne a kafar sada zumunta ta facebook.

Ga dukkan alamu Queen tana mayar da martani ne kan irin yadda ‘yam mata musamman na hausawa suke yawan amfani da dandalin Tiktok suna nuna tsaraici, tarexa yin rawar daba ta dace ba wanda a yanzu sun mayar da TikTok wajan sheke ayar su.

Sabida haka ne Queen take cewa, za’a iya kyale su duk da su masu hijabi ne a aje a auri ‘yam matan Tiktok din duk da irin tabargazar da sukeyi aikatawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button