Labarai

Sai da yayi tsawon watanni a wajan ‘yan bindiga sannan aka kai musu kudin fansa Naira 500,000 suka sake shi

Har yanzu dai ‘yan bindiga basu daina sace mutane suna ajiye su a wajan su ba har sai an fidda rai da su, wanda yanzu haka muka sami labarin wani bawan Allah wanda ‘yan bindigar suka sace shi sannan kuma suka ajiye shi a waja su har na tsawon wasu watanni.

Mutumin mai suna “Muktar Ibrahim” ya gamu da wani tsautsayin ya fada hannu ‘yan bindiga tun a watan Nuwamba a titin Kaduna-Abuja, sai a wannan lokacin ne Allah ya kubutar da shi.

Tun kusan tsawon wata biyu da wasu kwanaki Muktar Ibrahim yake tsare a hannun ‘yan bindigan ana ta maganar yadda za’a biya kudin fansa.

Kamar yadda “Daily Nigerian” ta ruwaito cewa, tun da farko dai ‘yan bindigar suka bukaci a biya naira miliyan 50 kudin fansa amma kuma hakan bai yiwu ba.

Sannan kuma Premium times sun ruwaito cewa, iyalan Muktar tare da ‘yan uwan sa suka cigaba da roko da tattaunawa da ‘yan bindigan tun a wancan lokacin har suka amince da naira 500,000.

Haka dai iyalan Muktar tare da ‘yan uwan nasa suka yi ta rokon ‘yan bindigar domin su rage kudin fansar har suka amince da’a biya naira 500,000.

Bayan haka ba iya kudin fansar ba kawai ‘yan bindigar sun saje fadin cewa, a hada musu da kiret din giya guda 6 da na Power Horse guda 1 sannan kuma da babura guda biyu.

‘Yan uwan Muktar tare da iyalan nasa sun shiga cikin halin damuwa inda har suke cewa, yaya zasu yi da kyar suka iya siyo kiret shida na giya da kuma sauran abin da ‘yan bindigar suka suka bukata.

Wani dan uwan muktar wanda ya bukaci a sakaya sunan sa sabida tsaro ya kara da cewa, ‘yan bindiga sun gargade su da cewa kada su kuskura su saka wani abu da za’a fallasa inda suke ko kuma su saka guba a cikin giyan da zasu kai musu.

Sannan dan uwan Muktar ya kara da cewa, Ko bayan da suka kai musu abubuwan da suka bukata cikin wani kungurimin daji, basu saki Muktar ba sai da suka tabbatar giyar babu matsala.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button