Duk binciken da aka gudanar akan “DCP Abba Kyari” ba’a same shi da laifin komai ba, Daga Joseph B. Donald
Shahararran marubucin nan Datti Assalafiy ya wallafa wani dogon bayani a shafin sa na kafar sada zumunta Facebook akan cirewa “DCP Abba Kyari” da aka yi daga kan mukamin sa, kan zargin sa da aikata wani laifi inda ya wallafa bayanin kamar haka.
Wannan sako ne mai muhimmanci garemu
‘yan Nigeria domin mu lura da wasu miyagun ‘yan jaridu wanda wakilan masu aikata miyagun
laifuka suka dauki nauyinsu, domin su cigaba
da yada labarun karya da batanci akan sarkin
yakin Nigeria wato “DCP Abba Kyari” irin su jaridar Sahara Reporters, People is Gazette, Punch News da dai sauran su.
Sannan Akwai wani labarin karya wanda wasu gidan jaridu suke yadawa tun satin da ya gabata akan “DCP Abba Kyari” da hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta kasa wato “Police Service Commission” da maigirma ministan shari’a, da kuma rundinar ‘yan sandan Nigeria suna ta juya bayanin hukumar kula da aikin ‘yan sanda domin su yada sharri da batanci akan ” DCP Abba Kyari”.
Bayan haka a cikin sakon takarda da hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta kasa ta rubutawa rundinar ‘yan sanda ta bayyana cewa, muddin idan ba’a kawo hujja akan “DCP Abba Kyari” ba to babu wani tuhuma akan sa, domin duk tsananin binciken gaskiya da aka gudanar akan “DCP Abba Kyari” ba’a same shi da aikata laifin komai ba, don haka hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta bada wa’adin sati biyu domin a kawo hujja imba haka ba zata wanke “DCP Abba Kyari” daga dukkan zargin da ake masa.
Duk wani binciken duniya an gudanar akan “DCP Abba Kyari” amma ba’a same shi da wani laifi na cin amana ba, kuskure ne guda daga wanda ba wani abu bane akwai aikin da ya yi wanda bai sanar da shugaban ‘yan sanda IGP ba, da kuma bayyana kokarin kare kan sa da ya yi a shafin sa na kafar sada zumunta facebook ba tare da amincewar IGP ba, sannan kuma lokacin da aka fara yada labarin batanci akan “DCP Abba Kyari” wannan shine kawai dan kuskuren da aka samu a tare da shi amma ba laifi bane.
Har ma mutane suna mamaki kan cewa, binciken da aka gudanar akan “DCP AbbaKyari” yayi tsanani da yawa ko farar hula ba’a masa irin wannan bincike, amma sai gashi sun tsananta bincike akan abokin aikinsu duk da haka basu same shi da aikata laifin komai ba.
Batun karban cin hanci Naira Miliyan 8 daga Hushpuppi wanda aka danganta da “DCP Abba Kyari” ana ta yadawa a social media ba haka
abin yake ba yadda abin yake shine, wani mutumi ne dan kasuwa ya karbi Kudi Naira
Miliyan 8 daga gurin wani mutumi mai suna Morgan wanda yake zaune a Kasar Dubai ba, “DCP Abba Kyari” ne ya karbi kudin ba, mutumin ya bayyana a gaban kwamitin binciken “DCP Abba Kyari”.
Cikin mamaki ana kokarin yiwa “DCP Abba Kyari” sharri, inda kuma yayi bayanin abinda ya faru ya gabatar da shaida na transaction details.
Mutumin dan kasuwa ne da kansa ya tura
account number din sa ga Morgan mazaunin
Kasar Dubai ya tura masa kudi domin ya saya
masa wasu kayayyaki anan gida Nigeria, dan
kasuwar ya tura account number dinsa a ranar 4-4-2020 Morgan ya tura Naira miliyan 5 sannan a ranar 9-4-2020 ya sake tura masa Naira miliyan 3, ya zama Naira Miliyan 8, sunyi wannan cinikayya a tsakaninsu ba tare da sanin “DCP Abba Kyari ba”.
Mutumin ya bayyana cewa, bayan sati 6 da tura masa kudi sai aka samu matsala bai sayi kayan ba amma a ranar 20-5-2020 Morgan wanda yake da zama a Dubai din sai ya kawo karan mutumin gurin “DCP Abba Kyari” ta hannun Hushpuppi, tunda Morgan bai da nambar wayan “DCP Abba Kyari” sabida bai taba saninsa ba sai labari to shine sai ya tuntubi Hushpuppi ya turawa “DCP Abba Kyari” shaidar an tura kudi wa dan kasuwan Naira milyan 5 da kuma miliyan 3 domin Abba Kyari ya gudanar da bincike.
Sannan kuma dan kasuwan ya gabatar da nasa shaidar a gaban kwamitin binciken na “DCP Abba Kyari” kan cewa, tabbas shi ya karbi kudin Naira Miliyan 8 a cikin account dinsa sannan kuma ya tabbatar wa kwamitin binciken “DCP Abba Kyari”, cewa Morgan ne ya tura masa kudi ba Hushpuppi ba kamar yadda wasu miyagun jaridu suke yada labarin.
Sannan mutumin ya sake bayyana cewa, yayi mamakin yadda wasu jami’an FBI da wasu jaridu suke kokarin dorawa “DCP Abba Kyari” wannan transaction na kudi, kuma ya musanta cewa ta ya zai kasance Morgan ya tura masa kudi domin ya saya masa kaya ranar 4-4-2020, sannan a kawo karansa gurin “DCP Abba Kyari” ranar 20-5—2020 ya kasance an dorawa “DCP Abba Kyari” sharri irin wannan.
Kwamitin da ya binciki “DCP Abba Kyari” ya binciki wannan mutumi dan kasuwa wanda Morgan ya tura masa kudi Naira Miliyan 8 domin ya saya masa kaya, kuma kwamitin ya gano cewa tabbas mutumin bayanan da ya fada haka yake, kuma ya cire kudin a tsakanin sati guda da aka tura masa a watan 4 na shekarar 2020.
Bayan haka ya kashe kudin gaba daya ba tare da ya bawa “DCP Abba Kyari” ko kobo ba sabida bai taba sanin ” DCP Abba Kyari” ba sai a lokacin da aka kai karansa sannan alkawarin da Hushpuppi ya yi a karan kansa a watan 1 na shekarar 2020 cewa, zai yiwa wasu mayakan rundinar “IRT” ihsani wanda suka je har jihohi hudu neman wani mai suna “Vincent Kelly” wanda ake zargi da aikata manyan laifukan yanar gizo, wanda Kwamitin binciken ” DCP Abba Kyari” suka gano.
A hiran da Hushpuppi yayi da “DCP Abba Kyari” ta WhatsApp an gudanar da tsatsauran bincike ba’a ga inda Hushpuppi ya tura wani abu ba a matsayin ihsani kamar yadda yayi alkawari, sannan kuma ya gagara cikawa yaran “DCP Abba Kyari” sun kama Vincent Kelly sun bincikeshi duk a tsakanin sati 4 tare da samun izni daga wata Kotu a Nigeria.
wanda Kotu itace ta bada izni wa rundinar “IRT” ta cigaba da tsare Vincent tare da bincikarsa bisa laifukan yanar gizo guda 20 da ya amince ya aikata, tare da abokinsa Hushpuppi da sauran mutanensu ‘yan damfara wanda suke zaune a Kasar Malaysia “Cyprus da South Africa”.
“DCP Abba Kyari” ya gabatar wa kwamitin da ya bincikeshi hujja cewa, duk bayanan hiransa da Hushpuppi da sukayi a WhatsApp da ake yadawa a kafofin sada zumunta aiki ne na bincike domin ya binciko hallayya da dabi’un
Hushpuppi da sauran mutanensa, domin ya jawoshi gida Nigeria ya kamashi tunda sakamakon binciken Vincent ya nuna masa
cewa shima Hushpuppi mai laifi ne abin zargi
da tuhuma wanda ya cancanta a kamashi a
bincikeshi, sai dai matsalar ba’a Nigeria yake
da zama ba.
A watan June 2020 lokacin da aka kamashi a
Dubai babu wata shaida da ta tabbatar da cewa “DCP Abba Kyari” yana da alaka na cin amana
tsakaninsa da Hushpuppi, Abba Kyari bai taba neman kobo daga Hushpuppi ba kuma duk binciken duniya da aka gudanar akan “DCP Abba Kyari” ya tabbatar da hakan bai da alakar banza da Hushpuppi ba.
Inda ace jami’an FBI sun tuntubi Gwamnatin Nigeria a sirrance da aka basu dama sun tattauna da mutumin nan dan kasuwa wanda Morgan ya tura masa kudi Naira Miliyan 8 domin su gano cewa ko mutumin yana da alaka da “DCP Abba Kyari” jarumin dan sanda wanda ya sadaukar da rayuwarsa, ya yaki masu garkuwa da mutane ya kubutar da dubbanin mutane har da ‘yan kasar Amurka mazauna Nigeria da akayi garkuwa da su a Kaduna, wanda hakan yasa hukumar FBI ta Amurka ta karramashi da lambar yabo a shekarar 2018.
Hushpuppi yaso “DCP Abba Kyari” ya daure abokinsa Vincent bisa laifin fashi da makami don ya shafe shekaru masu yawa a gidan yari, kamar yadda aka gani a hiran da Hushpuppi yayi da “DCP Abba Khari” a lokacin da “DCP Abba Kyari” yake kokarin jansa da zance sabida ya masa dabara ya jawoshi gida Nigeria ya kamashi ya bincikeshi ba tare da shi Hushpuppi din ya fahimci haka ba.
Don haka cikin wayo da dabara sai “DCP Abba
Kyari” ya bada belin Vincent a matsayin cewa bai da lafiya alhali ba haka bane dabara ne, inda ace “DCP Abba Kyari” yana bukatar kudi daga gurin Hushpuppi to da ya lakawa Vincent laifin fashi da makami ya kaishi kuto an daureshi shekara da shekaru kamar yadda Hushpuppi ya bukata.
To amma baiyi hakan ba sai dai “DCP Abba Kyari” ya bada belin Vincent, wannan ne dalilin da yasa Hushpuppi bai yiwa dakarun “IRT” ihsani kamar yadda yayi alkawari ba, bayan sun sha wahala sun ziyarci jihohi hudu wajen neman Vincent.
Duk wani babban mutum dan kasuwa ko kuma dan siyasa a Nigeria da ya je Kasar Dubai idan
Hushpuppi ya sami labari sai ya nemi ya
gana da shi, idan kuma ya samu dama sai ya
dauki hoto dashi akwai hotunan Hushpuppi
da manyan ‘yan siyasar Nigeria birjik a kafar sada zumunta ta yanar gizo.
Don haka wannan kira ne ga ‘yan Nigeria akan cewa, suyi watsi da labarun karya wanda wasu gidan jaridun da aka dauki nauyinsu suke yadawa akan “DCP Abba Kyari”, kar ku yadda da wani labari na batanci akan “DCP Abba Kyari” ku jira sanarwa a hukumance daga hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta kasa ko rundinar ‘yan sandan Nigria.