Labarai

Professor Yemi Osibanjo yana zawarcin daukar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Gidan Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa alamu masu karfi sun nuna Professor Yemi Osibanjo yana zawarcin daukar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya masa Mataimakin shugaban kasa a zaben da za’a gudanar shekara 2023.

An hango wasu manyan manyan wakilan Mataimakin shugaban kasa Professor Yemi Osinbajo sun yi wata ganawar sirri da tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso akan siyasar da za’a gudanar a shekarar 2023.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa gidan jaridar Daily Trust cewa wakilan Osibanjo sun gana da Kwankwaso domin su dawo dashi cikin jam’iyyar APC da manufar ya yiwa Osibanjo Mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

majiyar ta shaida cewa yanzu haka magana tayi karfi a tsakanin wakilan Osibanjo da Kwankwaso, kamar yadda wani makusancin Kwankwaso ya tabbatar wa gidan jaridar Daily Trust.

Idan APC ta tsayar da Osibanjo, yana daga cikin dabarun da jam’iyyar zatayi domin ta cigaba da mulki shine ta zabo wani babban mutum mai daraja da tarin masoya a Arewacin Nigeria, irinsu Maigirma Ministan Sadarwa Professor Isa Ali Pantami Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Malam Nasir El-Rufai da makamantansu a matsayin Mataimakin shugaban Ć™asa.

DAGA Datti Assalafiy yayi fatan Alkhari akan wannan lamari da ake tunain zai faru.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button