Uncategory

Subhanallah: Yan bindiga sunyi dirar miki sun aika mutum sama da 30 lahira.

Yan bindiga sunyi dirar mikiya cikin wasu kanan hukumomi a jihar ta zamfara sun kuma halaka mutun sama da 30 lahira sanan kuma wasu daga ciki sun jirkata.

Yan tada kayar bayan sun kai wannan harine sabida mazauna kanan hukumomi sun gaza basu kudi naira miliyan 40 da suka ka-kaba musu.

Maharan sun kai harin wadannan kauyikan kaman haka karamar hukumar Tsafe, Nasarawar Mai Fara, Yar Katsina, Karamar hukumar Bungudu da Kauyen Nasarawa dake Karamar hukumar Bakura.

Idan masu bibiyar mu basu mantaba Yan bindiga sun kakabawa mazauna kauyen wasu miliyoyin kudi da zasu biya kaman haraji.

Gogarma Ada Aleru ne ya saka wa mutanen wannan Kauyika harajin dole. Wanda da basu iya biya ba kuma ya aika da su lahira ya kuma sace matayen su da yawa ya nausa da su cikin daji.

Cikin kauyen yar Katsina maharan sun tarwatsa matasa sun kuma halaka mutun goma nan dake.

Wani Mai’aikacin lafiya ya shaidawa gidan jaridar Premium Times A lokacin da abun ya faru shima yana cikin kauyen. ma’aikacin yace abin dai ba’a cewa komai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button